Daga Auwal Adam Hukumomin kasar Saudiyya sun kaddamar da kisan wani matashi mai shekara 26 a duniya bisa zarginsa da halartar z...
Daga Auwal Adam
Hukumomin kasar Saudiyya sun kaddamar da kisan wani matashi mai shekara 26 a duniya bisa zarginsa da halartar zanga-zangar kin jinin gwamanti, kamar yadda hukumomin kare hakkin bil'adama suka tabbatar.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Mustafa al-Darwish ne a cikin watan Mayun 2015. Hukumomin kare hakkin bil'adama a ranar Talata sun bayyana cewa kafin a kaddamar da kashe matashin ba a sanar da ko iyayensa ba.
Kafar watsa labarai ta Reprieve ta labarto cewa; ma'aikatar tsaron cikin gida na Saudiyya ta bayyana cewa Mustafa al-Darwish mai shekara 26 an yanke masa hukuncin kisa kuma an kashe shi.
Iyayen Al-Darwish sun tabbatar da cewa ba a sanar da su cewa za a kashe dansu ba. Kawai suma sun ji labarin kashe dan na su ne a kafafen watsa labarai na zamani.
Hukumomin Saudiyya sun zargi Al-Darwish da shiga zanga-zangar kin jinin gwamnati, sai dai kafar watsa labarai ta Reprieve ta ce lokacin da ya halarci zanga-zangar yana da shekara 17 ne a duniya. Inda suka ce bayan an kama shi an killace shi aka rika azabtar da shi "har sai da ya fita hayyacinsa a lokuta da dama", inji majiyarmu.
Majiyar ta ci gaba da cewa; "domin dakatar da azabtar da shi da aka rika yi, sai ya amsa laifin da ake tuhumarsa".
Hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, tun kafin kashe Al-Darwish ta nemi hukumomin Saudiyya su dakatar da batun kashe shi a makon da ya gabata, inda ta ce; "Al-Darwish shi ne mutum na karshe da hukumomin za su kashe ba tare da yi masa adalci ba ta hanyar amfani da hujjar da suka samu a yayin azabtar da shi", inji su.
Majiyarmu ta Reprieve ta ce duk da cewa Mustafa Al-Darwish ya musanta zargin da ake yi masa a gaban kotu harma ya jaddada cewa ya amsa laifin ne saboda azabtar da shi da aka rika yi, amma kotun ta yanke masa hukuncin kisa.
Iyayen Al-Darwish sun ce sun shiga halin damuwa da kunci tun bayan kama dansu. "Muna rayuwa cikin kuncin da damuwa', inji su.
Sun ci gaba da cewa; "ta ya ya za su kashe yaro saboda sun ga hoto a wayarsa?" Inji iyayensa a sakon da suka aikawa majiyarmu.
Iyayen Al-Darwish sun ce an kama Mustafa ne da abokansa biyu a Tarout shekaru 6 da suka gabata, inda daga baya aka sake shi ba tare da zarginsa da komai ba. "Amma 'yan sanda suka ci gaba da rike wayarsa. Daga baya mu ka fahimci akwai wani hoto a wayarsa da ya batawa hukumomin rai. Inda suka kira mu daga baya cewa Mustafa ya zo ya karbi wayarsa, amma a maimaikon su ba shi, sai suka garkame shi, daga nan rayuwar kuncin mu ta fara", iyayensa suka tabbatar.
Ali al-Dubaisy, Daraktan kungiyar kare hakkin bil'adama ta 'European Saudi Organization for Human Rights' ya ce kashe Mustafa Al-Darwish ya nuna yadda ake kashe masu kananan shekaru a kasar; "kuma alama ce dake nuna cewa akwai munafurci a batun Mohammed Bin Salman na batun yi wa tsarin gudanar da kasar kwaskwarima", inji shi.
Al-Dubaisy ya ce har wala yau hakan na nuni da cewa batun soke dokar kashe kananan yara a kasar "zancen banza ne kawai", ya nusasshe.
No comments