SHEKARU 23 DA RASUWA: Jami'ar MAAUN Ta Mika Sakon Ta'aziyarta Ga Iyaan Tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Janar Sani Abacha


Hukumar Gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University dake kasar Jamhuriyyar Nijer, Nijeriya, Togo da kasar Faransa na mika sakon ta'aziyyarta ga daukacin iyalan tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha  kan cikarsa shekara 23 da rasuwa. Allah ta'ala ya yi wa Marigayi Janar Sani Abacha cika wa a rana irin ta yau 8 ga watan Yunin 1998. "Da fatan Allah (T) ya jikansa ya jaddada Rahma a gareshi", inji sanarwar Jami'ar MAAUN.  

Sanarwa sakon ta'aziyyar cika shekaru 23 da rasuwar na Janar Abacha na kumshe ne cikin wata takarda mai dauke da sanya hannun Ali Yusuf Kakaki, Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na Jami'ar ta MAAUN wanda aka raba ma manema labarai a yau Talata 8 ga watan Yunin 2021 a birnin Kano. 

Cikin sanarwar hukumar gudanarwa na Jami'ar ta Maryam Abacha American University ta ce rashin shugaban haziki kuma jarumi dan kishin kasa irin Marigayi Abacha  ba karamin babban rashi bane ga Arewa da kasar Nijeriya da daukacin Afrika ta Yamma baki daya. 

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa kasar Nijeriya ba za ta mance da irin ci gaban da mulkin Janar Abacha ya kawo mata ba, musamman gyaran manyan tituna, da bada magani kyauta a daukacin asibitocin kasa ta  hannun hukumar PTF. Haka kuma an samu ingantaccen tsaro lungu da sakon cikin kasar. 

Hukumar gudanarwa ta Jami'ar  ta MAAUN tana addu'ar Allah (SWA) ya jikan Janar Sani Abacha, ya kuma jaddada Rahma ga ruhinsa  ya kuma kyautata makwancinsa. 

Post a Comment

0 Comments