SHEKARU 60: Jami'ar MAAUN Ta Taya Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina MurnaShugaban rukunin jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) dake jamhuriyyar kasar Nijer da kuma Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin duniya, Hajiya Amina J. Mohammed murnar cika shekara 60 a duniya. 


A ranar Asabar din 26 ga watan Yunin 2021 ne mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin duniya, Hajiya Amina J. Mohammed ta cika shekara 60 a duniya. 


Sakon taya murnar na dauke ne a takardar da shugaba kuma mu'assasin Jami'ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu kuma ya aiko daga birnin Paris aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin. 


A cikin sakon taya murnar, Farfesa Abubakar Gwarzo ya ce gudummawar da Hajiya Amina ta bayar wajen ci gaban kasarta Nijeriya da nahiyar Afrika da ma duniya baki daya yana da yawa. 

Inda ya kara da cewa gudummawarta a bangaren jin kai da cimma muradun karni yana daya daga cikin dalilan da aka duba wajen ba ta mukamin ministar muhalli da gwamnatin Tarayya ta yi wanda daga bisani kuma majalisar dinkin duniya ta ba ta mukamin mataimakiyar Sakataren majalisar. 


"a madadin kaina da iyalina da kuma dukkanin hukumar gudanarwa na Jami'ar MAAUN, ina taya ki murnar cika shekara 60 a duniya", ya bayyana. 


Ya kara da cewa; "ina addu'ar Allah ta'ala ya kara miki koshin lafiya, tsawon rai cikin arziki wanda hakan zai ba ki damar ci gaba da bayar da gudummawa ga al'umma", inji Farfesa Abubakar Gwarzo a sakon taya murnar. 


Sakataren majalisar dinkin duniyar, António Guterres ya sake sabuntawa Amina J. Mohammed wa'adin mukaminta a matsayin mataimakiyar Sakataren majalisar bayan da shima aka kara masa wa'adin mulkinsa a karo na biyu a ranar Juma'a 18 ga watan Yunin 2021. 

Post a Comment

0 Comments