Suhaila Zakzaky: Ina Cikin Ƙuncin Rayuwa Kan Tsare Mahaifana Fiye Da Kwana 2,000Iyalan jagoran ƙungiyar Ƴan uwa Musulmi a Nijeriya, Malam Ibrahim el-Zakzaky sun nemi gwamnatin ƙasar ta sakar musu iyaye bayan da suka shafe fiye da kwana 2,000 a tsare a hannun hukumomi.

A wata hira da BBC Hausa, Suhaila Ibrahim Zakzaky, ta ce ba su da wani buri da ya wuce su ga an saki mahaifansu sun sake rayuwa da su.

A ranar Alhamis 3 ga watan Yunin 2021 ne Malam Ibrahim ya cika kwana 2,000 a hannun gwmanatin Najeriya, tun bayan kama shi da aka yi tare da matarsa a Disamba na 2015 a gidansa da ke Zaria a jihar Kaduna.

Tun daga wancan lokacin mabiyansa suke ta kira ga gwamnati da ta sake shi, musamman bayan bayar da belinsa da kotu ta yi.

"Babban fatanmu shi ne a sake su, tun da shi kansa laifin da aka ce an riƙe su a kai to an saki duk wani da ake tuhuma da shi, an ce saboda babu hujja.

"To don me kuma za a ci gaba da riƙe su da aka ce su suka sa a aikata laifin?" a cewar Suhaila.

Ta ƙara da cewa a yanzu ma an kai matakin da ba a barinsu su ga iyayens nasu akai-akai kamar a baya.

Sannan ta yi ikirarin har yanzu akwai raunuka na harbinsu da aka yi lokacin da aka je tsare su da ba su warke ba, "kuma ba a mayar da hankali wajen ba su kulawar da ta dace ba."

"Rayuwarmu (ƴaƴansu) cikin waɗannan kwanakin na tattare da tashin hankali da wahala saboda raba mutum da iyaye ba za a iya haɗuwa a lokacin da ake so ko nkulawa da su ba, abin tashin hankali ne.

"Balle su a irin yanayin da aka ɗauke su," ta ƙara da cewa.


Me Harkar Musulunci ta ce bayan kwana 2,000 da tsare Zakzaky?

A wata sanarwa da mabiya Harkar Musulunci  ta aike wa manema labarai ranar Talata 8 ga watan Yuni ma ta ce, bai kamata ƴan ƙasar da dama su yi gum da bakinsu kan kamen da gwamnatin Najeriya ta yi wa shugaban nasu ba.

Shugaban sashen yaɗa labaran Harkar ta Musulunci, Malam Ibrahim Musa da ya sa hannu a sanarwar ya ce: "Muna ganin shirun da mafi yawan ƴan Najeriya suka yi kan rashin adalci da zaluncin da ak yi wa Sheikh Zakzaky a matsayin abu mafi rashin dacewa a tarihin ƙasar.

"Shirunsu kan wannan babban rashin adalcin ba shi da maraba da masu goyon bayan hakan Ya kamata ƴan Nakeriya su gane cewa idan ka yi shiru kan lamari na rashin adalci, to fa kana goyon bayan waɗanda suke zalinci ne," a cewar sanarwar.

Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam'ian tsaro a Zariya.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Najeriya ta bayar da izinin fita da Sheikh Zakzaky Indiya don neman magani, sai dai kwanansa uku kacal ya koma kasarsa yana mai zargin cewa ba a bar shi ya ga likitocinsa ba.

Post a Comment

0 Comments