Suhaylat Na Zafafan Hawaye: Wa Za Ya Share Mata? -Ra'ayin Kamal Y. IyantamaKo da a ce ban yi wani bayani ba, kai da ganin fuskar wannan yarinya, za ka ba kanka amsar cewa lallai akwai wani abu muhimmi. Hausawa ma na ji suna cewa " labarin zuciya a tambayi fuska ". Wannan kam haka yake, ba wai a zance ne kadai ba.

Wannan baiwar Allah Suhaylat, daya ce daga cikin 'ya'yan mahaifanta da suka rage a raye, tun bayan wani al'amari marar dadin ji da ya faru, kuma ya yi sanadiyyar rasa rayukan 'yan uwanta.

Fiye da kwanaki dubu biyu (2000) mahaifi da mahaifiyar wannan yarinya, wato Malam Ibrahim Zakzaky da Malama Zinatuddenn, suna a tsare, a cikin yanayi na tsananin rashin lafiyar da likitoci ne kadai za su iya tantance yanayinta. Duk da an sha yin kiraye-kirayen a sake su, musamman mabiya  (almajiran) wannan Malami. Na taba ji ma har kotu ta bayar da umarnin sakin su, amma gwamatin Tarayya ta ki bin umurnin yin hakan. Wata kotun ma ta ba damar su fita kasar waje domin zuwa neman magani. Har sun fita din, amma aka yi kumbiya-kumbiyar da ta sa ala tilas suka dawo ba a duba lafiyarvtasu ba. Ina ji kamar har yanzu ba su samu wannan dama ta sake sakin su zuwa neman magani ba. 

Da a ce za a ba Suhaylat damar cewa; a saki iyayenta ita kuma a rike ta, kafin a karasa wannan tambayar za ta ce EH! Saboda tsananin bala'in takaicin da ke kunshe a cikin zuciyarta, na azabar kadaicin rashin Iyayenta.

Har ga Allah ina cikin tausaya wa wannan yarinya Suhaylat, irin halin da take ciki na kukan zahiri, da azababben kukan zuci. Da ina da yadda zan yi, da na yi sanadiyyar bada damar a saki Iyayenki kanwata, illa dai kawai har gobe ina mai taya ki wannan juyayi, da ya yi silar barci ya yi hannun riga da kwayar idaniyarki.

" DUK MAI IMANI, DOLE YA TAUSAYA WA SUHAYLAT "

Sannan ina mai ba ki shawarar ki ci gaba da yin addu'a, kamar yadda na yi yak'inin kina yi, haka ni ma ina taya ki fatan ganin Iyayenki sun samu 'yanci. Allah Yana Gani, Allah Yana Ji!

Ga Dai Suhaylat Na Zafafan Hawaye, Wa Za Ya Share Mata?

Kamal Y. Iyantama
( Artist / Cartoonist / Mawaki / Marubuci )
17th June, 2021.
0706 548 4046.

Post a Comment

0 Comments