TA FARU TA KARE: Gobe Gwamnan Zamfara Zai Koma Jam'iyyar APC


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

 
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle Maradun ya kammala shirinsa tsaf na ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC a gobe talata.

Kwamishainan yada labarai na jihar Zamfara kuma Shugaban babban Kwamitin yada labarai na bikin canza shekar, Honorabul Ibrahim Magaji Dosara ya tabbatar da hakan a kafafen yada labarai na jihar Zamfara.

 
Tun a watan da ya gabata ne Gwamnan Matawalle ya rushe majalisar zartarwarsa baki daya da kuma duk wani me mukamin siyasa da ya nada, tun daga nan ne al'umma ke ta hasashen cewa, lallai zai canza shekar daga jam'iyyar PDP da koto taba kujerar gwamna zuwa jamiyyar APC da kotun koli ta amshe wa kujerar sakamakon rashin yin zaben fidda gwani. 

Post a Comment

0 Comments