Ta'ammali Da Muggan Kwayoyi Ya Fi Matsalar Tsaro Hatsari, Inji Shugaba Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya  ce tasirin ta’ammali da muggan kwayoyi a kasar ya fi rashin tsaro muni.

Shugaban ya yi wannan bayanin ne  yayin bikin kaddamar da yaki da ta’ammali da kwayoyi a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja a ranar Asabar.

An kaddamar da wannan yakin ne a ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don yaki da safara da shan muggan kwayoyi.

Shugaban wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ya umurci hukumar yaki da muggan kwayoyi da ta samar da wani shiri da zai kunshi al’ummomi, da zummar kaddamar da aikin lalata gonakin wiwi da wuraren sarrafa kwayoyi, musamman kudu maso yammaci da kudu maso mkudancin kasar.

Post a Comment

0 Comments