Tattaunawa Ce Kadai Za Ta Magance Matsalolin Nijeriya, Inji Gbajabiamila


 
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce tattauanwa ce kadai za ta magance tarin matsaloli da kalubalen da ke addabar Najeriya.

Ya bayyana haka ne ranar Asabar a sakonsa na taya murna kan ranar Dimokradiyya ta 2021.

Kakakin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Lanre Lasisi Najeriya ta fuskanci sauye-sauye da ci gaba ta bangarori da dama, musamman ta bangaren ayyukan raya kasa da kuma yancin fadin albarkacin baki tun bayan dawowarta kan tsarin mulkin Dimokradiyya a shekarar 1999.

Gbajabiamila ya kuma jinjinawa ’yan Najeriya wadanda ya ce sun bayar da gagarumar gudunmawa ga shugabanni a cikin shekaru 20 din da suka gabata, tare da yin kira gare su kan su ci gaba da bayar da hadin kan.

Ya ce kowacce kasa a duniya na fama da irin nata kalubalen, inda ya ce Najeriya ma ba a barta a baya ba.

Sai dai ya ce duk da haka, har yanzu tsarin mulkin Dimokradiyya shine zakaran gwajin-dafi a tsakanin kasashe.

Kakakin ya kuma ce tattauanwa ita ce hanya daya tilo wajen magance kowacce irin matsalar da ake fama da ita a kasa.

Post a Comment

0 Comments