Tsohon Sakataren Jam'iyyar APGA Na Kasa Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC A ZamfaraDaga Hussaini Ibrahim, Gusau

Sakataren Jami'yyar APGA na kasa, kuma dan takarar kujerar gwamna a jam'iyyar a zaben da ya gabata na 2019, Alhaji Sani Abudullahi Wamban Shinkafi ya koma jam'iyyar APC a Zamfara.

Alhaji Sani Abudullahi Wamban Shinkafi, ya bayyana cewa ya kwashe sama da shekaru sha Tara yana cikin jam'iyyar APGA, ya kuma rike mukamai tun daga mataki na jiha har ya zuwa Sakatare na kasa, amma bai taba yin tunanin zai canza jam'iyyar ba; "sai yau ga shi na koma jamiyyar APC", inji shi. 

A cewarsa Wanban Shinkafi, ya kuma tabbatar da cewa: "lokaci ya yi na in dawo gida jihar Zamfara dan na bada gudummuwa ta ta ci haban jihar. Don haka na aminta da kiran da gwamna Bello Matawalle da yi mani na inda fa masa wajen amsa kiran shugaba kasa da ya yi masa na ya koma jam'iyyar APC domin ci gaban jihar", inji Wanban Shinkafi.

Wanban Shinkafi ya kuma tabbatar da cewa ba dan neman mukami ba ne ko kujera daga gwamna Bello Matawalle ko dan neman abin duniya ba ne dan Allah ya ba shi duk abin da yake ba mutum na rufin asiri. 

Shugabannin jam'iyyar APGA na kananan hukumoni da gunduma sun bi shi zuwa APC a fadin jihar.

Post a Comment

0 Comments