Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tura Ta Kai Bango: Gwamnan Zamfara Ya Bai Wa Al'umma Umurnin Kare Kansu Daga Harin 'Yan Bindiga

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau A ci gaba da bukukuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin gwamnan Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawall...Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

A ci gaba da bukukuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin gwamnan Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawalle Maradun ya bai wa al'ummar jihar damar kare kansu daga harin 'yan ta'adda, 'yan Bindiga da  masu garkuwa da mutane.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a wajen wa'azin mako-mako da gwamnatin ke gabatarwa a kowacce Juma'a.

Kuma ya kara da cewa, gwamnatin ta yi iya kokarinta na ganin an kawo karshe wadannan 'yan ta'adda abin ya ci tura, sai kara yawaita abin yake yi. "A don haka na bada umurnin kare kai a duk lokacin da aka ji cewa mahara za su kawo muku hari a  kauyukan ku", inji gwamnan.

Gwamnan Matawalle ya kuma tabbatar da cewa, duk dan ta'adda da aka kama ko mai bai wa maharan rahotan sirri ya tabbatar sai dai uwarsa ta haifi wani.

Matawalle ya kara kalubalantar 'yan adawar siyasa akan cewa, idan suna kaunar al'ummar jihar Zamfara su fito su bayyana wa al'umma cewa, ba su da hannu ko jindadi da hare-haren da ake wa al'umma jihar Zamfara, inji gwamna Matawalle. 

No comments