Twitter: Ba Za Mu Bari Shafukan Sada Zumunta Su Haddasa Rikici Tsakanin Al'ummarmu Ba - Buhari
Shugaba Buhari ya ce dole shafukan sada zumunta su dauki alhakin ayyukansu. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dakatar da shafin Tuwita ne saboda yada labaran karya da ke iya haddasa rikici a kasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Sehu ya fitar ranar Asabar, ya ambato Shugaba Buhari yana cewa dakatar da Tuwita ba kawai martani ne ga goge sakonsa ba, har ma da "jerin matsalolin da shafukan sada zumunta suke da su a Najeriya, inda suke yada labaran karya da ke da mummunan tasiri."

A cewarsa, dole shafukan sada zumunta su dauki alhakin abubuwan da suke haddasawa.

"Dole ne manyan kamfanonin sadarwa su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu. Ba za a bari su ci gaba da taimakawa wajen yada kalaman addini, da wariyar launin fata da kiyayya da kuma karya ba wadanda ka iya haddasa rikicin tsakanin al'umma, lamarin da zai kai ga rasa rayuka. Hakan zai iya wargaza wasu kasashen," in ji Shugaba Buhari.


Ya kara da cewa kalaman da ya yi da ke gargadin masu tayar da hankula a yankin kudu maso gabashin kasar ba ba barazana ga kowa, yana mai cewa abin takaici ne da Tuwita ya goge su.


Dalilin da ya sa Twitter ya goge saƙon Buhari
Ya kara da cewa kalaman da ya yi da ke gargadin masu tayar da hankula a yankin kudu maso gabashin kasar ba sa barazana ga kowa, yana mai cewa abin takaic ne da Tuwita ya goge su.

Shugaba Buhari ya ce ya dade yana gargadi kan matakan shafukan sada zumunta na raba kan jama'a.


Bidiyo: Me goge saƙon Shugaba Buhari da Tuwita ya yi ke nufi?

Sai dai a sanarwar da ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar a yammacin Asabar, ya soki matakin gwamnatin Shugaba Buhari ya dakatar da shafin Tuwita yana mai cewa hakan tamkar take hakkin fadin albarkacin baki ne.

"Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da 'yancin fadin albarkacin baki. Matakin da gwamnati ta dauka a baya bayan nan na dakatar da Tuwita take 'yancin fadin albarkacin baki ne," in ji sanarwar.

A cewar Amurka, matakin ya aike da sako maras kyau ga 'yan kasa da masu zuba jari da 'yan kasuwa.

"Kamar yadda Shugaba Biden ya fada, bukatarmu ta bayyana ra'ayin kowanne mutum, da yin muhawara a bainar jama'a da yin komai a fili su ne manyan jarinmu. Hanyar da kawai Najeriya za ta zama mai tsaro ita ce ta bari a yi sadarwa mai yawa, ba kadan ba, tare da daukar matakai na hakika wajen hadin kai, da zaman lafiya da dorewa," in ji sanarwar ta ofishin jakadancin Amurka.

A ranar Juma'a ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin na Tuwita a matsayin martani ga matakin da wasu suke ganin na goge sakon Shugaba Buhari da kamfanin ya yi ne.


-Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments