Twitter Ya Goge Saƙon Jagoran ƴan Biafra Nnamdi Kanu


Kamfanin Twitter ya goge ɗaya daga cikin sakwannin jagoran kungiyar 'yan a ware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Twitter ya goge saƙon jagoran na IPOB a shafin da ke ɗauke da sunansa wanda ba tantance ba inda yake yin barazana ga sojojin Nijeriya idan har aka tura su yankin kudu maso gabashi.Twitter ya ce saƙon ya saɓa dokokinsa.

Wannan na zuwa bayan gwamnatin Nijeriya ta toshe Twitter ga ƴan ƙasar.

A ranar Talata ne Twitter ya goge ɗaya daga cikin saƙon shugaba Buhari tare da cewa ya saɓa dokokin Twitter kamar yadda Bbc ta labarto. 

Post a Comment

0 Comments