Ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma


Ƙungiyar ma’aikatan shari’a a Nijeriya ta janye aikin aikin gama-gari da ta tsunduma.

A cewar Jaridar Daily Trust, Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da shugabannin ƙungiyar da kuma Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a Najeriya NJC ƙarƙashin jagorancin Alƙalin alƙalai Mai shari’a Ibrahim Muhammad.

Tun a farkon watan Afrilu ƙungiyar ta shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da wasu buƙatunta da suka shafi cin gashin kai a jihohi.

Hakan na nufin za a buɗe kotuna a Najeriya bayan shafe tsawon biyu a rufe bayan janye yajin aikin.

Post a Comment

0 Comments