Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Wani Matashi Ya Tattara Komatsansa Ya Fice Daga Jam'iyyar APC A Zariya

Daga Auwal Adam   MADOGARA ta labarto cewa; wani matashin dan siyasa wanda ake gogayya kafada da kafada da shi a cikin jam'...


Daga Auwal Adam 

MADOGARA ta labarto cewa; wani matashin dan siyasa wanda ake gogayya kafada da kafada da shi a cikin jam'iyyar APC ta karamar Hukumar Sabon Gari dake jihar Kaduna, ya shelanta ficewarsa daga jam'iyyar bisa abin da ya kira da jam'iyyar na yi na; "sakamakon rashin adalci, tsari, danniya, handama, babakere da mulkin kama karya da ta ke yi wa Ƴaƴanya da ta haifa. Ba zan tsura ido ana zaluntar Al'umma ba na yi shiru, saboda kare muradun jam'iyya", ya wallafa. 

Matashin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a shafinsa na Facebook, inda ya fara da cewa; "Ni Shiek Umar Kwangila halastaccen Ɗan Jam'iyyar APC Mai Mulki. Daga yau 17th June, 2021 ina jaddada ficewa ta daga Jam'iyyar APC, sakamakon rashin adalci, tsari, danniya, handama, babakere da mulkin kama karya da ta ke yi wa Ƴaƴan ta da ta haifa. Ba zan tsura ido ana zaluntar Al'umma ba na yi shiru, saboda kare muradun jam'iyya", ya tabbatar. Ya ci gaba da cewa; "A karshe ina nisanta kai na da duk wani abu da ya danganci APC tun daga Gunduma har Ƙasa baki Ɗaya, kuma ina ƙara shaidawa Al'umma wannan hukunci na yanke shi ne bisa ƙwararan dalilai, kuma mutumci da zumuncin da ke tsakanin mu da wasu Ƴaƴan jam'iyyar APC ya na nan kama yadda ya ke, amma zan ɗauki mataki akan duk wanda ya alƙanta Ni da APC", ya jaddada. 


1 comment