Shugaban Majalisar wakilan Nijeriya, Femi Gbajabiamila yace ya zama dole a samar da dokokin da zasu takaita wuce gona da iri da ake samu w...
Shugaban
Majalisar wakilan Nijeriya, Femi Gbajabiamila yace ya zama dole a samar da
dokokin da zasu takaita wuce gona da iri da ake samu wajen amfani da kafofin
sada zumunta wadanda ke yin illa a cikin kasa.
Gbajabiamila
ya ce Majalisar dokoki ta dade tana nazari akan daukar matakan da suka dace
wajen samar da irin wadannan dokokin da zasu kare jama’a daga illolin wadannan
kafofi amma sai ta dinga jan kafa saboda korafin da jama’ar kasar keyi dangane
da fargabar hana jama’a bayyana ra’ayoyin su ko kuma fadin albarkacin bakin su.
Shugaban
Majalisar wanda ya amince da ci gaban da kafofin suka samar, ya kuma bayyana
cewar sun zama wata kafa na haifar da illa daga wasu masu amfani da su ta
hanyar da bata kamata ba.
Gbajabiamila
yace kasashen duniya da dama yanzu haka na daukar irin wadannan matakai na
sanya dokokin da zasu tabbatar da ingancin wadannan kafofin sada zumunta da
kuma wadanda zasu bada damar ladabtar da wadanda suka saba ka’ida.
Dan
majalisar yace hakkin su ne su kare ko wane dan Najeriya kuma hakan za su yi
wajen gabatar da dokokin da zasu taimakawa jama’a baki daya.
Yunkurin
daukar irin wannan mataki na samar da dokokin da zasu kare masu amfani da
wadannan kafofi da kuma hukunta wadanda suka wuce gona-da-iri ya gamu da suka a
majalisar da ta gabaci wannan.
Matsalolin
da aka samu lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda da kuma rikicin
gwamnatin Najeriya da kamfanin twitter ya sake bada damar gabatar da sabon
yunkuri daga Majalisar na yunkurowa domin gabatar da dokar da ta dace.
No comments