‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Awon dake Yankin Kachia ta Jihar Kaduna inda suka hallaka mutum guda tare da sa...
‘Yan bindiga
dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Awon dake Yankin Kachia ta Jihar
Kaduna inda suka hallaka mutum guda tare da sace mutum 12.
Sarkin Kachia
Idris Suleiman ya ce maharan sun fara kai hari ne wani gidan biredi a kauyen
Awon inda suka hallaka mutum guda da kwashe wasu mutane 5, yayin da daga bisani
suka kara gaba inda suka kwashe wasu mutane 28 a bakin kasuwa cikin su harda mace
guda mai dauke da juna biyu.
Suleiman ya ce
bayan kashe mutum guda da kuma kama wasu da suka yi garkuwa da su, ‘yan
bindigar sun kuma saci kayan dake shagunan mutane bayan sun gudu domin tsira da
rayukan su.
Kakakin ‘yan
Sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce
maharan da suka kai harin na dauke ne da muggan makamai.
A sanarwar da ya
rabawa manema labarai Jalige ya ce dakarunsu sun bi bayan ‘yan bindigar inda
suka kubutar da mutane 2, yayin da ake ci gaba da farautar su domin kubutar da
sauran.
‘Yan bindigar da
suka addabi yankin arewa maso yammacin Nijeriya na ci gaba da kai hare-hare a
wasu sassan jihar Kaduna inda suke kashe fararen hula da kuma garkuwa da wasu
domin karbar kudin fansa.
Daga cikin
wuraren da ‘yan bindigar ke kai hari yanzu haka bayan tare hanya suna kwashe
fasinjoji harda makarantu inda suke dibar dalibai kamar yadda aka gani a
Kwalejin aikin noma da Jami’ar Greenfield a baya bayan nan, bayan na Jihohin
Katsina da Neja da kuma Kebbi.
No comments