Yadda 'Yan Bindiga Suka Sace Dalibai Mata 30 A Yawuri Ta Jihar Kebbi


Rahotanni daga Jihar Kebbi sun ce akalla dalibai 'yan mata 30 'yan bindiga suka sace lokacin da suka kai hari makarantar Sakandaren mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yawuri.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce majiyoyi sun shaida mata cewar 'yan bindigar sun kai harin ne akan babura daga dajin Rijau da ke jihar Niger yau da asuba, inda suka fi karfin jami’an tsaron da ke gadin makarantar.

Jaridar ta ce majiyar ta ta shaida mata cewar bayan dalibai mata 30 da aka sace, 'yan bindigar sun kuma kwashi malamai guda 3 sun gudu da su.

Wannan shi ne hari na 3 da ake kai wa makarantun Najeriya a cikin makwanni 3 bayan wanda aka samu a makarantar Islamiyar Tegina a ranar 30 ga watan Mayu, wanda har yanzu ba’a kubutar da daliban ba da na makarantar fasahar Nuhu Bamalli da ke Jihar Kaduna.


Post a Comment

0 Comments