Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Mutum 51 A Zamfara


‘Yan bindiga sun kashe mutane akalla 51 yayin jerin hare-hare da suka kai kan wasu kauyukan karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce, garuruwan da ‘yan bindigar suka afkawa sun hada da Saulawa, Askawa, Kadawa, Kwata, Maduba, da kuma Ganda Samu.

Bayanai sun ce hare-haren sun tilasta wa daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara tserewa zuwa cikin garuruwan Dauran da kuma Zurmi, inda a yanzu haka suke gudun hijira.

Wasu da suka tsira da rayukansu sun ce adadin ‘yan bindiga da dama ne haye kan babura suka afkawa garuruwan nasu, inda nan take suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Post a Comment

0 Comments