'Yan Bindiga Na Neman Mamaye Masarautata, Inji Sarkin ZazzauMai martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan yadda matsalar tsaro ta yiwa masarautarsa dabaibayi.

Rfi Hausa ta labarto cewa Mai Martaban ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin tawagar kwamishin tsaron jihar Kaduna da lamuran cikin cikin gida Samuel Aruwan a jiya Litinin, inda Sarkin na Zazzau ya ce ‘yan bindiga sun yiwa al’ummarsa kofar rago, abin da ya sanya ba su da damar iya yin barci cikin kwanciyar hankali a cikin birnin na Zazzau da kewaye.

Ambassada Ahmad Nuhu Bammali ya ce halin da masarautar Zazzau ke ciki ba abin da za a lamunta bane, ganin yadda suke fama da matsala ta hare-haren ‘yan bindiga duk da kasancewar hedikwatocin manyan hukumomin tsaron Nijeriya a kusa da su.


A baya-bayan nan ne dai ‘yan bindiga suka sace wani adadi na dalibai da malamai daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya, kwana uku bayan haka kuma wani gungun ‘yan bindigar suka sace mutum 12 a Unguwar Sabuwar Gayan da Kofar Kona a dai garin na Zariya.

Post a Comment

0 Comments