'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Uku A Titin Kaduna Zuwa Zariya

 


Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum biyar a kananan hukumomin Chikun da Igabi dake jihar. 

Kwamishinan lura da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar. 

Aruwan ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun kashe mutum biyu a karamar hukumar Chikun tare da tarwatsa gini guda biyu da ya hada da wurin ibada. 

Kwamishinan har wala yau ya tabbatar da cewa; sauran mutum ukun an kashe su ne a Lambar Zango dake titin Kaduna zuwa Zariya a karamar hukumar Igabi. 

Ya tabbatar da cewa gwamnan jihar, Nasir El-rufai ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa ran na su, inda ya yi rahama gare su. 


Post a Comment

0 Comments