Daga Muhammad Farouk MADOGARA ta labarto cewa waÉ—ansu 'yan bindiga sun harbe Malamin Jami'ar Benin dake jihar Edo. Mala...
Daga Muhammad Farouk
MADOGARA ta labarto cewa waÉ—ansu 'yan bindiga sun harbe Malamin Jami'ar Benin dake jihar Edo. Malamin Jami'ar wanda yake karantarwa a bangaren sha'anin mulki na Jami'ar an kashe shi ne a ranar Asabar.
Malamin mai suna Maxwell Eseosa Aimuen, mai shekaru 33 ya fara aiki a Jami'ar ne a shekarar 2015.
Jaridar Standard Gazette ta tabbatar da cewa an kashe shi ne a gidansa dake Isiohor a birnin Benin City dake jihar ta Edo.
Maxwell Eseosa Aimuen an harbe shi ne a daidai lokacin da yake kokarin shiga gidansa a cikin mota. Inda 'yan bindigar suka harbe shi a wurare da dama kafin su gudu.
Har yanzu babu cikakken bayani kan dalilan da ya sanya suka kashe shi.
Majiyarmu da ta tuntubi Jami'ar hulda da Jama'a na Jami'ar Dr Benedicta Ehanire, ta tabbatar da faruwar lamarin.
No comments