Mutumin dake zama a kauyen Babban Maye Tunga Rogo Dutsin Nasarawa yace mutane 26 aka kashe a kauyen su tsakanin Sallar la’asar zuwa Magariba ba tare da wani ya kai musu dauki ba.
Shaidar gani da idon yace duk da yake akwai jami’an tsaro a Nasarawa da Anka babu guda da yaje domin taimaka musu a lokacin da ake kai musu harin, yayin da Yan bindigar suka hana mutune kwashe gawarwakin ‘Yan uwan su da aka kashe domin yi musu jana’iza.
Mun yi iya bakin kokarin mu domin jin ta bakin Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Shehu Mohammed amma abin yaci tura, domin yace ya zuwa lokacin da muka tintibe shi bai samu labari ba daga jami’an su dake Yankin amma kuma zai bincika.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar Yan bindiga barayin shanu dake kasha mutane ba tare da kaukautawa ba.
0 Comments