‘Yan Bindiga Sun Kona Asibiti, Motar ‘Yan Sanda Da Kashe Mutum 5 A Katsina'Yan bindiga masu tarin yawa dauke da muggan makamai sun kai sabon farmaki a garin Zandam dake a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Kamar yadda majiyar mu dake a garin ta tabbatar, 'yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Litinin.

Majiyar ta Katsina Post ta ci gaba da cewa yayin harin, 'yan bindigar sun kona wata asibitin mata masu ciki da kananan yara da ake cikin ginawa da kuma motar ‘yan sanda.

Hakazalika sun kuma kashe akalla mutane biyar cikin su harda dan sanda daya.

Haka kuma harin na 'yan ta’addar ya yi sanadiyyar jikkatar mutane shida wadanda yanzu haka suna asibiti suna jinya.

Post a Comment

0 Comments