'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamai Da Kashe Dalibin Nuhu Bamalli Polytechnic A ZariyaDaga Muhammad Farouk

Waɗansu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kari hari Makarantar kimiyyah da fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic dake titin Zariya zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da mata da 'ya'yan Malam Ahmad Abdul (Stat) tare da sace Malamai guda biyu da ya hada da; Habila Nasai da kuma Malam Adamu Shika. 

Har wala yau 'yan bindigar sun yi awon gaba da dalibai uku da ba a kai ga tantance su ba ya zuwa hada rahoton nan. 

Sannan sun harbi dalibai biyu kamar yadda ganau ya shaidawa MADOGARA, sai dai daya daga cikin daliban da aka raunata ya mutu da safiyar yau Juma'a 11 ga watan Yunin 2021. 

Dalibin mai suna Ahmad yana ajin karshe (HND II) yana karantar bangaren kididdiga (statistics). 

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Alhamis 10 ga watan Yunin 2021 da misalin karfe 11 na dare, inda suka rika ruwan luguden wuta har na fiye da awa daya. 


Sai dai bayanai sun nuna cewa da safiyarnan Matar Malam Ahmad da 'ya'yansa an sake su da safen nan. 

Post a Comment

0 Comments