YANZU-YANZU; Aisha Buhari Ta Goge Shafinta Na Twitter Domin Goyon Bayan Mijinta

 


Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta goge shafinta na Twitter bayan da ta sanar da cewa za ta yi hakan da yammacin ranar Juma’a. 

 ‘zan goge shafina na Twitter a wannan lokacin. Ki yi tsawon rai gwamnatin Tarayyar Nijeriya’, ta rubuta kafin ta goge shafin na ta a Twitter. 

Matakin da Uwargidan shugaba Buhari ta dauka na zuwa ne bayan da gwamnatin Nijeriya ta ayyana haramta amfani da shafin Twitter a fadin kasarnan. 

 ‘Yan Nijeriya a yau Asabar sun tashi ba sa iya amfani da shafin na Twitter. Sai dai ta barauniyar hanyarnan ta hanyar amfani da manhajar dake boye sirruka wato (VPN Virtual Private Network). 

Wanda amfani da wannan dabarar ke ba  su damar amfani da Twitter din, domin manhajar ga duk mai amfani da ita ba ya nuna mutum na Nijeriya ne. 


Post a Comment

0 Comments