Rahotanni sun bayyana cewa kamar takwararsa Twitter, shima shafin sada zumunta na Facebook ma ya goge rubutun da shugaban kasa, ...
Rahotanni sun bayyana cewa kamar takwararsa Twitter, shima shafin sada zumunta na Facebook ma ya goge rubutun da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi na cewa zai yi maganin masu tada kayar baya a Nijeriya.
Ibo sun yi zargin cewa, Shugaban kasar da su yake inda suka kaiwa Kamfanonin Facebook da Twitter karar Shugaban kan kalaman na sa, lamarin da ya sanya shafin Twitter ya goge kalaman Shugaba Buhari kafin daga bisani shima Facebook ya goge kalaman shugaban.
Gwamnatin Tarayya a yau Juma'a ta bayyana cewa ta dakatar da shafin Twitter na har sai abin da hali baki daya a Nijeriya tun bayan goge rubutun na shugaban kasa.
Gwamnatin ta ce ana amfani da shafin na Twitter wajen yada kalaman da ke kawo kiyayya da fitina a kasar.
No comments