YANZU-YANZU: Gwamnan Bauchi Ya Sauke Dukkanin Masu Rike Da Mukaman Siyasa Na Jihar


Labarin dake shigoga MADOGARA da safen nan na nuni da cewa; Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Abdulkadir ya sauke dukkanin kwamitin zartaswa na jihar ciki harda Sakataren gwamnati da kuma shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar da ma dukkanin kwamishinonin jihar da masu ba shi shawara. 

Sanarwar sauke dukkanin masu rike da mukamin siyasar na dauke ne da sa hannun Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai, Mukhtar Gidado, wanda ya fitar a yau Laraba 9 ga watan Yunin 2021, inda ya bayyana cewa gwamnan ya nemi dukkanin kwamishinonin jihar da aka sauke su mika ragamar lura da ma'aikatar ta su ga Babban Sakataren ma'aikatar. 

Sai dai gwamnan ya ce wadanda bai sauke ba sun hada da mai ba shi shawara kan harkokin kafafen watsa labarai, da na tsaro da na zuba jari da kuma na majalisar jihar. 

Inda gwamnan ya mika godiyarsa ga kafataninsu bisa ayyukan da suka gabatar a yayin rike mukaman. Tare da yi musu fatan alheri kan abin da za su fuskanta a gaba. 


            Kwafen takardar dakatarwar. 

Post a Comment

0 Comments