YANZU-YANZU: An Kashe Dalibi A Jihar Kaduna A Yayin Zanga-zangaWani dalibi a Kwalejin ilimi ta jihar Kaduna daje Gidan Waya, a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna ya rasa ransa sakamakon harbinsa da aka yi. 


Marigayin da aka kashe yana tare da 'yan'uwansa dalibai ne da suke zanga-zangar karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi, a yayin da jami'an tsaro suka harbe shi a lokacin da suke son tarwatsa daliban. 


Daya daga cikin masu zanga-zangar da ya nemi a sakaya sunansa a yayin hira da jaridar Daily Trust ya ce; ssun fito zanga-zangar ne domin su kalubalanci karin kudin makarantar da aka yi a makarantun jihar inda suka yi kacibis da jami'an tsaro a wajen makarantar. 


Karin bayani na tafe. 

Post a Comment

0 Comments