YANZU-YANZU; Minista Malami Ya Bada Umurnin Hukunta Wadanda Suka Karya Dokar Haramta Twitter A Nijeriya


Ministan shari’a kuma Babban mai shigar da kara na gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya bayar da umurnin cafkewa tare da hukunta wadanda suka karya dokar haramta amfani da shafin Twitter a Nijeriya da gwamnatin tarayya ta yi. 

Malami ya umurci ofishin shigar da kararraki na gwamnatin Tarayya (DPPF) dake karkashin ofishinsa da su yi gaggawar daukar mataki tare da fara daukar matakan hukunta wadanda suka karya dokar gwamnatin Tarayyar na hana amfani da Twitter a Nijeriya. 

Ministan ya bayyana hakan ne a sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin kafafen watsa labarai da hulda da jama’a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu ya fitar, inda Malami ya umurci ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, da hukumar lura da sadarwa ta kasa, NCC da sauran hukumomin gwamnati da lamarin ya shafa da su yi gaggawar daukar matakan da ya dace domin hukunta wadanda suka karya dokar da gwamnatin ta kafa ba tare da bata lokaci ba. 


Post a Comment

0 Comments