YANZU-YANZU: Twitter Ya Goge Gargadin Shugaba Buhari Ga IPOB


Shafin sada zumunta na Twitter ya goge rubutun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi akan 'yan tawayen IPOB inda yake gargadinsu da cewa mafi yawansu da suke kada gangar yaki a yau ba su san yakin basasar da ya auku a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 bane. Inda ya ce zai mayar musu da martani dangane da aika-aikar da suke yi a yau daidai da yaren da za su fi ganewa kamar yadda MADOGARA ta labarto. 


Jaridar People Gazette ta ce akwai yiwuwar shafin Twitter ya goge shafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma ya dakatar da shi na dan wani lokaci. 

Batun na shugaban kasar dai ya jawo cece-kuce a shafuka sada zumunta musamman Twitter, inda wasu suka yi Allah-wadai da kalaman na shugaban kasar a yayin da wasu suka goyi bayan kalaman shugaban kasar. 


Post a Comment

0 Comments