YANZU-YANZU: 'Yan Arewa Na Zanga-zanga A Abuja Suna Neman A Bai Wa Biyafara KasarsuDaga Muhammad Farouk


Gamayyar kungiyar mata a karkashin kungiyar 'Northern Women Associations' a yau Asabar sun gudanar da zanga-zanga idan suka nemi da a bai wa 'yan Kudu maso gabashin Nijeriya damar su kada kuri'a domin a ba su damar masu son kafa kasar Biyafara su zabi damar kafa kasar ko kuma su ci gaba da kasancewa a Nijeriya kamar yadda MADOGARA ta labarto. 


Shugaban gamayyar kungiyar, Hadiza Adamu ita ce ta bayyana hakan a madadin membobin kungiyar a yayin zanga-zangar a Abuja. 


Hadiza ta bayyana cewa tarihin Nijeriya ya nuna yadda mata suka sha wahalar yaki da masu tada kayar baya. "Mun ga hakan daga shekarar 1967 zuwa 1971, mazajenmu sun mutu sun bar mu da 'ya'ya mu kula da su bamu da komai. Sauran mazajen da suka rayu sun ci gaba da rayuwa, mu kuma muna wuri guda", inji ta. 

Jaridar Punch ta labarto Hadiza na ci gaba da cewa; "abin da ya biyo bayan yakin da tashin hankalin da muka fada ciki har yanzu yana zuciyoyinmu da jikkunanmu. A kan wannan muka hadu wuri guda a yau muna mai bayyana cewa ba mu son wani yakin ya sake barkewa daga ayyukan masu tada kayar baya", ta lurantar. 


"A don haka muna kira da babban murya ga shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na Uban kowa a kasarnan, da kuma shugabancin Majalisa, shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawal; Kakakin Majalisar Tarayya, Femi  Gbajabiamila da su yi kira ga kada kuri'ar raba gardama a kasarnan", ta bada shawara. 


Ta ci gaba da cewa; "a bai wa mutane damar su zabi su ci gaba da kasancewa a Nijeriya cikin zaman lafiya ko kuma su barta. Duk wata Kungiya ko wani dan kasa da yake so ya barta domin su ci gashin kansu kamar yadda 'yan kudu maso gabashin Nijeriya suke ta fafutikar ballewa daga Nijeriya, a bar su su barta cikin zaman lafiya ba tare da haddasa wani yakin basasar ba", inji ta. 


"A yau yankin Ibo sun maida kudu maso gabashin kasar kamar sansanin yaki. 'Yan arewa ba tare da la'akari da kabilarsu rayuwarsu na cikin hadari. Kayayyakin gwamnati na cikin hadari. Jami'an gwamnati daga 'yan sanda da soji na cikin hatsari. Haka zalika ofishin INEC da duk wani alami na dimokuradiyya a kasarnan ana lalata su a kowacce rana. Mazajenmu da suke zuwa huldar kasuwanci a kudu maso gabashin kasarnan ba su dawo gida cikin kwanciyar hankali. Shugabannin siyasarmu da ke zuwa kudu maso gabashin kasar domin gudanar da ayyukan kasa ana musu kisan gilla da rana tsaka", ta karkare. 

Post a Comment

0 Comments