YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Da Malamai A Jihar Kebbi


Bayanai daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai da dama daga Kwalejin Tarayya da ke garin Yawuri.

Ganau sun ce 'yan bindigar sun tafi da dalibai da yawa sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya gaya wa BBC cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar kana suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba daliban sannan suka tafi da su.

Wasu mutane sun ce an kai dalibai da dama asibiti domin yi musu maganin harbin bindiga sakamakon raunukan da suka samu yayin da suke tserewa daga harin na 'yan bindiga.

'Yan bindigar "sun ci karfin 'yan sandan Mobile da ke gadin makarantar wadanda sun fi 20, sun sassari wasu sannan suka harbi wasu. Akwai 'yan sandan da aka sara an tafi da su asibiti, yayin da su kuma 'yan bindigar suka wuce da wasu yara," in ji Muhammad Bello Ingaski.

Ya kara da cewa dalibai da dama sun tsere "duk run rarrabu cikin daji yanzu muna kokari mu tattaro su."

Sai dai ya ce ba a san yawan daliban da aka sace ba.


-Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments