Daga Shafiu Umar Rahotannin da ke shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; waÉ—ansu 'yan bindiga sun tare hanyar Bang...
Daga Shafiu Umar
Rahotannin da ke shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; waÉ—ansu 'yan bindiga sun tare hanyar Bangi zuwa Shadadi dake karamar Hukumar Mariga a jihar Neja, inda suka ci gaba da cin karensu ba babbaka.
Wakilinmu ya labarto mana cewa; ya zuwa hada rahoton nan 'yan bindigar na ci gaba da harbe-harbe, inda matafiya kuma suka tsaya suna jiran komai ya lafa kafin su wuce.
Sai dai har yanzu babu labarin garkuwa da mutane, raunata su ko kashewa.
No comments