Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Iran


A yau Juma'a al'ummar kasar Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ke gudanar da zaɓe domin zabar mutumin da zai gaji Shugaba Hassan Rouhani.

Jagoran juyin juya hali na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ne ya fara jefa kuri'arsa inda kuma ya yi kira ga jama'a su fita domin yin zaben. 

Bayanai na nuni da cewa ana ganin dan takara Ibrahim Ra'isi ne kan gaba a zaben inda tsohon gwamnan bankin kasar Abdolnasser Hemmati ke zama babban abokin hamayyarsa.

'Yan takara hudu ne ke fafatawa a zaben na yau. Inda uku ke da tsattsauran ra'ayi a yayin da daya ke da matsakaicin ra'ayi. 

Post a Comment

0 Comments