Bbc Hausa ta labarto cewa; a lissafi na tsakatsaki, an sace mutum 13 a kullum cikin wata shida na farkon shekarar 2021, a cewar wani binci...
Bbc Hausa
ta labarto cewa; a lissafi na tsakatsaki, an sace mutum 13 a kullum cikin wata
shida na farkon shekarar 2021, a cewar wani bincike da cibiyar SBM Intelligence
ta gudanar.
Jaridar
TheCable wadda ta ga rahoton binciken, ta ruwaito cewa an gudanar da binciken
ne daga watan Janairu zuwa Yuni.
Rahoton
ya nuna cewa an yi garkuwa da jumillar mutum 2,371 a jiha 36 ciki har da Abuja,
babban birnin ƙasar.
An samo
ƙididdigar ce daga rahotannin da kafofin yaɗa labarai ke bayarwa da kuma
manhajar bin diddigin harkokin tsaro ta Council of Foreign Relations.
'Yan
bindiga sun nemi naira biliyan 10 a matsayin kuÉ—in fansa ya zuwa 30 ga watan
Yuni. Sai dai bai bayyana ko nawa aka biya ba daga cikin kuÉ—in.
Rahoton
wanda ya ce an fi yawaita sace mutane a watan Fabarairu (605), ya bayyana JIhar
Neja a matsayin wadda aka fi satar mutanen inda aka yi garkuwa da mutum 643.
No comments