Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta yi kira da babbar murya, inda ta yi tir da Allah-wadaida ya...
Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta yi kira da babbar murya, inda ta yi tir da Allah-wadaida yanayi; "da aka zalunci babban Malamin addinin Musulunci da ke birnin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta hanyar yin amfani da makircin tsararriyar "Mukabala" da gamayyar Malaman Maja na jihar Kano, kafin daga bisani a kama shi ba bisa ka'ida ba, a kuma gurfanar da shi a gaban babbar Kotun Shari'ar addini da ke birnin Kano a ranar Juma'a 16 ga Yuli, 2021, ana tuhumar sa da aikata laifuka wadanda suka hada da batanci da cin mutunci ga Annabi da kuma sauran munanan laifuka. Bayan nan kuma aka tura shi ajiya zuwa gidan Yari, aka garkame shi har sai zuwa ranar 28 ga watan Yulin nan".
Harkar ta Musulunci da aka fi sani da 'yan shi'a ta bayyana hakan ne a sanarwar da Ibrahim Musa Shugaban Dandalin Sadarwa, Harkar Musulunci A Nijeriya ya fitar aka kuma rabawa manema labarai a ranar Litinin 19 ga watan Yulin, 2021.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; "Muna
bibiyar lamurran da suka shafi bambancin fahimtarsa ta addini da na wadannan
gamayyar Malaman Maja na Kano da kuma yadda gwamnatin da Ganduje ke jagoranta
ta dauki bangare ba ta hanyar rufe Makarantar Shehin Malamin da kuma
Masallacinsa ba tare da tun farko ta yi bincike domin tantance gaskiyar tuhumar
da ake yi masa ba. An ja shi zuwa ga yin "Mukabala" da gamayyar
Malaman Maja wadanda gwamnati ke goyon bayansu, lamarin da ya rikide, ya canza
zuwa shari'ar sirri, wadda wadanda ke kalubantar sa bisa son rai suka kasance
sune masu gabatar da kara kuma masu yanke hukunci a lokaci guda. Abin da aka
kira wai "Mukabala" ta bayyana a sarari cewa an tsara ta ne tun farko
domin a dadada wa Malaman Majar da ke kalubalantar wannan Malami da ake
tsangwama. An aiwatar da lamarin ne a bayan idanun jama'a a wurin da yake cike
da mutanen da ke tsananin ki da adawa ga Shehin Malamin".
"Hakazalika,
Jagoran "Mukabalar", Farfesa Salisu Shehu, daya ne daga cikin wadanda
suka gabatar da koke kan Shaikh Abduljabbar, kuma Bawahabiye/Basalafe ne na
gidi, wanda a fili ba ya boye adawarsa da kiyayyarsa ga Shaikh Abduljabbar
Nasiru Kabara da kuma karantarwa sa. Kuma kamar yadda aka zata, sai ga shi
Malaman Maja da kuma gwamnatin Ganduje dukkanin su sun bayyana cewa Shaikh
Abduljabbar ya gaza gamsar da su, kuma ya zama wajibi a hukunta shi, wasu ma
har da neman a zartar masa da hukuncin kisa!"
"Hakika
gajerun faya-fayan bidiyo na Gwamnan jihar Kano da Kwashinansa na harkokin
addini wadanda suka karade kafafen sadar da zumunci na zamani sun kara tona
asirin boyayyar manufa ta gwamnatin Kano da kuma makircin wadannan masu bakar
kiyayya da sunan gamayyar Malamai. Suna so ne kawai su sakaye Shaikh
Abduljabbar domin a daina jin sa da ganin sa, su kuma haramta karantarwarsa ta
addini da harkokinsa kawai saboda yana da sabanin fahimtar addini wanda ya
sabawa ra'ayin su. Mun yi amannar cewa gwamnatin Ganduje tana amfani ne ba bisa
dacewa ba da karfin mulki da iko domin murkushe Shaikh Abduljabbar, duk kuwa da
an san cewa yana gudanar da al'amuransa na karantarwar addini cikin lumana.
Masu yaki da shi kawai suna da tsananin rashin hakuri ne da wadanda suke da
bambancin fahimtar addini iri daya da su. Malaman Maja na Kano ya zama wajibi
su gane cewa bai dace su yi amfani da karfi wajen sanya sauran al'umma su bi
ra'ayinsu ko fahimtar su ba. Tabbas wannan a sarari take wa Shaikh Abduljabbar
'yancinsa ne na aikwatar da addini wanda Kundin tsarin Mulkin kasa ya tabbatar
masa a irin wannan kasa ta tarayyar Nijeriya wadda babu ruwanta da addini".
"'Yancin
da Kundin tsarin Mulkin tarayyar Nijeriya ya tanadar tare da tabbatar wa da
Shaikh Abduljabbar Kabara ya hada da 'yancin gudanar da addini, bayyana ra'ayi
da kuma 'yancin bauta wa Mahalicci, karantarwa, aiwatar da addini, da kuma
aikata karantarwar addinin da ya zaba wa kansa. Kamawa da gabatar da
tuhume-tuhume ga Shaikh Abduljabbar, wanda gwamnatin Kano karkashin Jagorancin
Abdullahi Ganduje ta yi ya ci karo tare da sabawa wadannan tanade-tanade na
Kundin tsarin mulkin kasa, don haka da babbar murya mun yi tir da Allah-wadai
da wannan mummunar dabi'a ta gwamnatin jihar Kano, kuma ya kamata dukkanin 'yan
Nijeriya ma'abota hankali da adalci su fito su bayyana rashin goyan bayansu da
rashin amincewarsu da wannan lamari abin ki da gwamnatin Ganduje ta aikata ba
tare da la'akari da bambance-bambancen sabanin fahimtar addini da ke
tsakankanin su ba".
Sun karkare da cewa; "Daga
karshe, muna kira ga Gwamna Ganduje da ya janye dukkanin wadannan zarge-zarge
na rashin kangado da ake yi wa Shaikh Abduljabbar, a kuma dawo masa 'yancinsa
wanda Kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi ba tare da bata lokaci ba. Shaikh
Abduljabbar yana da 'yancin bayyana fahimtarsa kamar yadda sauran Malam Majar
da ke kiyayya a gare shi suke wa'azinsu kamar yadda kowannen su ya fahimta" suka jaddada.
No comments