Akalla
mutane 25 ne suka rasa rayukan su a wata ambaliyar ruwa da ta faru a kasar
China, lamarin da ya raba mutane sama da dubu 2 da muhallan su. Inda wasu
hotuna da fayafayan bidiyo da aka rika yada su a kafafen sada zumunta sun nuna
yadda ruwa ya kaiwa mutane har wuya saboda yawansa tare da ruguza gidaje.
Ambaliyar
ruwan ta faru ne sakamakon ruwan sama kaman da bakin kwarya da aka rika
shekawa, wanda ya sanya madatsun ruwa da manyan koguna suka rika ambaliya.
Tuni
dai shugaban kasar Xi Jingping ya bayyana ambaliyar a matsayin mummunan tashin
hankalin da ya faru a kasar, yana mai cewa dole a dauki matakin gaggawa duk
kuwa da cewa lamarin na neman gagarar hukumomin bada agajin gaggawa na kasar.
Munin
ambaliyar ya tilastawa jami’an sojoji da na ‘yan sanda shiga cikin aikin ceto,
la’akari da yadda ambaliyar ta shafi sama da mutane miliyan 10.
Rahotanni
sun bayyana cewa rabon da a sami ruwan sama mai karfi da yawan na bana a China
tun shekaru 60 da suka gabata.
Babban
abin fargabar a yanzu shine yadda hukumomi a kasar suka bayyana cewa akwai
yiwuwar a sami ruwan saman da ya fi na yanzu yawa da karfi nan ba da jimawa ba.
0 Comments