Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Amurka Ta Fara Kwaso 'Yan Afghanistan

  DW Hausa ta labaro cewa; 'yan asalin Afghanistan 200 sun isa Amurka a wannan Juma'a. Ayarin mutanen na kunshe da 'yan Afghanis...

 


DW Hausa ta labaro cewa; 'yan asalin Afghanistan 200 sun isa Amurka a wannan Juma'a. Ayarin mutanen na kunshe da 'yan Afghanistan da suka yi wa sojojin Amurka ayyukan tafinta tare da iyalansu a zaman shekaru 20 da sojojin Amurka suka yi a kasar.

Da ma dai tun da farko gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi alkawarin tsugunnar da dubban 'yan Afghanistan da suka yi wa sojojin Amurka aiki kuma suke tsoron ka da a kai musu harin huce takaici a yanzu da Amurkan ta fara janye dakarunta a kasar. 

A cikin wata sanarwa da Joe Biden ya fitar ya ce mutanen da suka fara sauka Amurka a wannan Juma'a zangon farko ne na mutanen da Amurka ta kuduri aniyar dawo da su kasarta domin su rayu cikin kwanciyar hankali biyo bayan barazanar da suke fuskanta daga mayaka a Afghanistan.

Kawo yanzu dai kusan 'yan Afghanistan 20,000 ne da suka yi wa sojojin Amurka aikin tafinta ke bukatar Amurka ta ba su izinin shiga kasarta don tsira daga barazanar da suke fuskanta a cikin gida. 


No comments