An Fara Sauraron Shari'ar Sunday Igboho A Asirce A Kwatano

 


Kotu a kasar Kwatano ta ci gaba da sauraron karar jagoran ƴan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho a asirce a Cotonou.

An haramtawa ƴan jarida da magoya bayansa shiga kotun a cewar jaridar majiyarmu  ta Jaridar The PUNCH.

Sai dai magoya bayansa sun ce ba a tsangwamesu ko tilasta mu su fita daga harabar kotun ba.

A ranar Alhamis da ta gabata kotun ta ɗage sauraron karar Igboho zuwa ranar Litinin bayan lauyoyinsa biyar sun gaggara gamsar da masu shigar da kara.

Sai dai kotun ta saki matar Igboho da aka cafkesu a tare a hanyarsu ta tserewa zuwa Jamus.

Post a Comment

0 Comments