Rundunar
‘yan sandan Nijeriya ta kaddamar da bincike a game da zargin da ake yi wa
mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan kasar Abba Kyari, wanda Amurka ke zargi da
alaka da wani shahararren dan damfara Ramos Abbas da ake kira Hushpuppi da
yanzu haka ke tsare a hannun FBI da ke Amurka.
Shi
dai Hushpuppi, mai shekaru 37 a duniya, ya zargi Kyari da karbar makudan
kudaden don kame wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Chibuzo Vincent.
Sai
dai tuni Kyari ya musanta wannan zargi a shafinsa na Facebook, yana mai bayyana
cewa, bai karbi ko sisin kwabo ba daga hannun Hushpuppi.
Kyari
na cikin zaratan jami'an 'yan sandan Najeriya da suka yi fice wajen yaki da
miyagun laifuka a kasar, yayin da wannan batu na cin hanci da rashawa ya haifar
da cece-kuce a sassan kasar.
Wata
sanarwa da FBI ta fitar ta ce, Hushpuppi ya damfari mutane daban daban akalla
Dala miliyan 24, ciki kuwa har da wata Dala miliyan 1.1 da wani attajiri ya
ware domin gina makarantar kananan yara a Qatar.
0 Comments