Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ana Fargabar Bullar Nau'in Cutar Polio Mai Saurin Yaduwa A Nijeriya

  Rfi Hausa ta labarto cewa; Hankula ya tashi a Nijeriya bayan fargabar sake bullar cutar Polio nau’in cVDPV2 mai saurin yaduwa da aka samu ...

 


Rfi Hausa ta labarto cewa; Hankula ya tashi a Nijeriya bayan fargabar sake bullar cutar Polio nau’in cVDPV2 mai saurin yaduwa da aka samu a jihohin kasar 13 tare da Abuja babban birnin Kasar.

Masana sun alakanta sake bullar cutar ta Polio bayan tun farko WHO ta wanke kasar kan yadda mutane ke kin karbar allurar rigakafin da kuma kin kammala alluran kariya da iyaye ke kin kai yaransu.

Yayin da kwayar cutar Polio ta WPV ke matsayin kan gaba wajen yada nau'in cutar ta cVDPV da ke da saurin bazuwa bayanai sun ce yanzu haka Najeriya na fama da yaduwar nau’in wanda ke matsayin babbar barazana.

Masana kiwon lafiya a Najeriyar sun ce sake bullar cutar ta polio tashin hankali ne da kuma barazana dai dai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen lafiya kala-kala.

Cikin watan Yunin 2020 ne Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta wanke Najeriyar daga jerin kasashen da ke fama da cutar ta Polio ko da ya ke dama Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar sake bullar cutar a kasar mai yawan jama'a miliyan 200.

Babban daraktan hukumar kula da Lafiya a matakin farko na Najeriya Dr Faisal Shu’aib ya ce nau’in sabuwar Polio mai saurin yaduwar ta bayyana a jihohin Abia da Bayelsa da Borno da Delta.

Sauran jihohin sun hada da Jigawa da Kano da Kebbi da  Lagos da Jihar Niger baya ga Rivers da Sokoto da Yobe sannan jihar Zamfara kana babban birnin Najeriyar Abuja.


No comments