Ƙarin Ɗalibai Uku Sun Kuɓuta Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kaduna


Bbc Hausa sun labarto cewa; Ɗalibai uku na makarantar sakandaren Bethel Baptist High School a Kaduna sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa ɗaliban sun tsere ne daga wani sansanin da ake tsare da su tun a ranar 19 ga watan Yulin 2021.

Wata ƴar uwar ɗaya daga cikin ɗaliban da ta bayyana sunanta da Funmi, ta shaida cewa ɗaliban uku sun shafe kwana biyar suna yawo a daji kafin su hadu da makiyaya da suka taimaka wajen nuna musu hanyar fita.

Sannan ɗaya daga cikinsu bayan shiga gari ya rike lambar mahaifinsa don haka sai ya yi aro waya ya kira babansa domin ya zo ya mai do su gida.

An gano wadanan dalibai a yammacin Lahadi bayan sako ɗalibai 28 da ƴan bindigar suka yi.

Post a Comment

0 Comments