Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Kama Ni EFCC Ta Yi Ba -Saraki

  Ofishin Yada Labarai na Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa ba kama Saraki EFCC ta yi ba.  Ofish...

 


Ofishin Yada Labarai na Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa ba kama Saraki EFCC ta yi ba. 

Ofishin a wata takardar manema labarai da Shugabanta, Yusuph Olaniyonu ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa da kansa Saraki ya ziyarci ofishin na EFCC.

Sanarwar ta fara da cewa; "Ofishin Yaɗa Labarai na Dr. Abubakar Bukola Saraki na son bayar da tabbacin cewa, yau da rana, Dr. Saraki bisa raaɗin kansa ya ziyarci ofishin Hukumar EFCC domin bayar da bayani ga wasu tambayoyi da hukumar ke son jin amsarsu daga gare shi.

"Idan za a iya tunawa bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya a Abuja, bisa kiyaye haƙƙin ɗan adam wanda Dr. Saraki ya shigar a gabanta a zamanin tsohon shugaban hukumar ta EFCC, inda kotun ta hana hukumar ci gaba da bibiyarsa har sai komi ya bayyana a fili. Hukumar a zaman kotu na ranar 14 ga watan Yulin 2021 ta sanar da alƙali cewa wannan odar ta kotu tana hana ta gudanar da aikinta.

"Bayan wannan ƙorafi da EFCC ta yi wa kotu ne, a matsayinsa na ɗan ƙasa managarci, Dr. Saraki bisa zaɓinsa ya ziyarci hukumar domin bayar da amsa ga duk wata tambaya da suke da ita a kansa.

"Da yammacin yau ya ziyarci ofishin hukumar a yau da rana inda suka yi masa tambayoyi, ya kuma ba su amsa. Tuni kuma ya dawo gida. Ba kama shi aka yi ba.

"Dr. Saraki ya sanar da hukumar cewa, babu wani abu da yake ɓoyewa, kuma a shirye yake ya bayyana a gabanta don amsa duk wata tambaya da suke da ita gareshi."


No comments