Bayan Rahoton Jaridar MADOGARA, Masarautar Zazzau Ta Soke Bukukuwan Sallah

 


Daga Ammar Muhammad

Jaridar MADOGARA a rahoton ta na safiyar yau Litinin ta yi hasashen cewa; akwai yiwuwar a soke hawan babbar sallah a masarautar Zazzau biyo bayan  shawarar da kwamitin yaki da cutar korona na gwamnatin Tarayya a karkashin Ofishin Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha ta bayar saboda dawowar cutar a karo na uku samfurin Delta.

Kwamitin yaki da korona ta bayyan jihohi bakwai dake fuskantar hadarin cutar ciki kuwa harda jihar Kaduna.

Bayan bullar rahoton MADOGARA, kwatsam da ranar yau Litinin, Masarautar Zazzau ta bada sanarwar cewa; Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli da majalisarsa sun yi taro sun tsayar da shawarar cewa; “an  soke hawan Babban Sallah na bana da aka shirya za a  gudanar a ranar Talata 10 ga watan  Zulhijjah,  1442 daidai da 20 ga watan Yulin 2021. Saboda haka ba za a gudanar da hawan sallah ba”, inji sanarwar.

Masarautar ta bayyana dalilai biyu da suka sanya  aka soke hawan wanda ta ce; “an soke hawa saboda dalilai na rashin tsaro da kuma matsala da ta taso na al’amarin cutar mai sarke numfashi (COVID-19 Pandemic)”, suka nusasshe.

Sai dai masarautar ta ce za a gudanar da sallar idi Babba kamar yadda aka saba a dukkanin masallatan da aka saba a kasar ta Zazzau.

“Mai Martaba  Sarkin Zazzau na umurtan dukkanin Hakimai masu kasa da su yi sallah Babba a gundumarsu tare  da jama’arsu. Ana kira da a ci gaba da kiyaye dokokin cuta mai sarke numfashi. A kuma ci gaba da yiwa kasa addu’ar zaman lafiya, da fatan Allah ya kawo mana karshen wadannan  fitintinu dake addabar kasar mu, Amin”, inji takardar.

Alhaji Barau Musa Aliyu, Sarkin Fulanin Zazzau, kuma Sakatare na masarautar shi ne ya sanya takardar hannu kuma aka aikawa dukkanin Hakimai dake karkashin masarautar.


Kwafen Takardar


 

Post a Comment

0 Comments