Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) tare da Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta HURIWA sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, da ya sauka daga kujerarsa ta saboda ta’azzarar matsalar tsaro a jihar.
A cewarsu, kiran ya biyo bayan yadda gwamnan ya gaza sauke nauyi a matsayinsa na shugaban tsaro a jihar da kuma kin yin sulhu da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane jihar.
A ranar Litinin dalibai 26 ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar Bethel Baptist, Maraban Rido, karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Shugaban CAN, reshen Kaduna, Reb. Joseph Hayab, wanda babban malamin cocin Baptist ne, ya yi bayanin cewa daliban dake zaune a dakunan kwana kafin a yi garkuwar su 180 ne, ya kara da cewa: ‘mun kirga su da safiyar nan (Litinin) kuma ba a ga mutum 174 ba.
Ya bukaci gwamnan da yayi murabus, idan ba zai iya magance matsalar tsaro a jihar ba.
0 Comments