CIKIN HOTUNA: Masu Zanga-zangar Kafa Kasar Yarbawa Sun Fita Duk Da Jibge Jami'an Tsaro

 


Al’umma da dama masu rajin kafa kasar Yarbawa sun fita zanga-zanga a garin Legas.

Zanga-zangar wacce kungiyar Ilana Omo Odua ta kafa kasar Yarbawar ta kira a yau Asabar ya samu halartar al’umma duk da kokarin dakatar da zanga-zangar da jami’an tsaron ‘yan sanda suka yi. 

Majiyarmu ta ce da misalin karfe 9 na safe al’umma suka fara taruwa a Gani Fawehinmi Park dake Ojota a Legas, din. 

Sai dai tuni tun kafin su bayyana aka jibge jami’an tsaro a wurin wanda ya hada da jami’an ‘yan sanda, da kuma soji cikin shirin ko ta kwana. 

Masu zanga-zangar dai na dauke da riguna da takardu da tutoci dake alamta ballewa daga Nijeriya tare da kafa kasar su ta Yarbawa inda suke rera wakokin dake alamta hakan. 

“kasar Yarbawa kawai muke bukata”, inji masu zanga-zangar. 


Ga wasu kadan daga cikin hotunan da muka samu daga majiyarmu: 


Post a Comment

0 Comments