Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikin Shekaru An Yi Garkuwa Da Sarakuna 113 A Nijeriya

Rfi Hausa ta labarto cewa; akalla Sarakunan gargajiya  113 ne masu satar mutane don karbar kudin fansa suka sace a Nijeriya  a cikin shekaru...


Rfi Hausa ta labarto cewa; akalla Sarakunan gargajiya  113 ne masu satar mutane don karbar kudin fansa suka sace a Nijeriya  a cikin shekaru 4 da suka gabata, a cewar wani nazari da jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa  a Nijeriya ta yi , lamarin da kwararru ke cewa zai iya durkusar da masarautar gargajiya  a kasar.

A ranar 11 ga watan Yuli  nan ‘yan bundiga suka sace Alhaji Alhassan Adamu, sarkin Kajuru, a jihar Kaduna kuma suka nemi kudin fansa na naira miliyan 2 a kan sarkin mai daraja ta 2 mai shekaru 85 bayan ya shafe sa’o’i 24 a gun ‘yan bindigar.

Zalika a makon da ya gabata ‘yan bindiga suka sace sarkin Jaba, Kpop Ham, Malam Danladi Gyet Maude mai shekaru  sama da 80, shi ma sai da ya kwana a gun  su.

Wannan al’amari na faruwa ne akasari a arewacin kasar, musamman arewa maso yammaci.

Kadan daga cikin sarakuna da aka yi garkuwa da su a baya can

A shekarar 2018, a yankin Anchuma, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sarkin Ikulu a watan Janairu, a kann kudin fansa da yak ai Naira miliyan 1.

 Zalika a ranar 6 ga watan Mayu, barayin sun sace Alhaji Umar Awoje, Hakimin Gulida a babban birnin Tarayar Najeriya a kan kudin fansa da ya tasamma naira miliyan 10.

A jihar Taraba, sarkin Sansani, Mallam Abdulmudallabi Nuhu da wasu mutane 2 sun shiga hannun wadanna ‘yan bindiga a kan hanyar Jalingo zuwa Mutum Biyu, kuma sai da aka biya kudin fansa na Naira miliyan 50.

Shi ma mai Martaba sarkin Ogodor a jihar Delta, Sunday Olisewokwu, ya fada hannun masu satar mutanen a yankin  Eri-Onicha-Olona a ranar 3 ga watan Yuni, kuma sun nemi naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa.

Haka kuma a kan hanyar Auga-Ise Akoko ta jihar  Ondo aka kama Olori Olukemi Agunloye,  mai dakin sarkin Auga Akoko community  da direbanta, kuma an biya naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa.

Haka lamarin ya yi ta tafiya har ya zuwa yanzu.


No comments