Da Yiwuwar A Dakatar Da Hawan Sallah A Masarautar Zazzau

 


Daga Ammar Muhammad

Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnonin jihohin arewacin kasar, Sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su dakatar da bukukuwan hawan Sallah babba domin dakile yaduwar annobar Korona da gwamnatin Tarayyar ta ce tana kokarin dawowa da karfinta.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin yaki da annobar Korona na Nijeriya, Boss Mustapha ne ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi a birnin Tarayya Abuja.

Matakin gwamnatin Nijeriyar dai ya biyo bayan sanya jihohi shida da kuma birnin Abuja cikin matakin tsaurara matakan dakile yaduwar Korona, annobar da wasu kwararru kan sha’anin lafiya ke gargadin yiwuwar sake barkewarta a zango na uku, idan ba a dauki matakan da suka dace ba.

Jihohin da lamarin ya shafa dai sun hada da Legas, Oyo, Kano, Filato, Kaduna, Ribas da kuma birnin Tarayya Abuja.

Masarautar Zazzau dai dake jihar Kaduna na daya daga cikin masarautun dake shirin gudanar da Hawan Sallah a bana, amma ganin wannan sanarwa ta kwamitin dakile yaduwar cutar korona ta gwamnatin Tarayya, wadansu na hasashen cewa hakan na iya tilasta a soke hawan sallar da aka shirya gudanarwa  ganin yadda gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai na daya daga cikin  gwamnonin dake  yaki da cutar korona tun bayan  bullarta a Nijeriya a cikin watan Fabarairun 2020.


Hawan Sallah a masarautar ZazzauPost a Comment

0 Comments