Daliban Islamiyyar Tegina Sun Cika Makwanni Shida A Hannun 'Yan Bindiga

 


Yayin da aka shiga mako na 6 da sace daliban makarantar Islamiyyar Malam Tanko Salihu su 136 a garin Tegina na jihar Neja a Tarayyar Najeriya, wasu bayanai sun ce iyaye da ‘yan uwan daliban har zuwa yanzu sun gaza tattara kudin fansar da ‘yan bindigar suka bukata yayinda gwamnati a bangare guda ta yi watsi da koke tare da kiraye kirayen ganin ta taimaka wajen kubutar da yaran.

Jaridar Nijeriya ta Daily Post ta ruwaito cewa duk da matakin sayar da wani bangare na makarantar da kuma yadda iyayen daliban ke ci gaba da sayar da gidajen da su ke ciki, har zuwa yau Naira miliyan 30 ta gaza haduwa don kubutar da yaran.

Tun farko ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da yaran sun bukaci fansar Naira miliyan 200 gabanin mayar da shi Naira miliyan 150 kafin sake ragewa zuwa miliyan 110 kana suka mayar da shi miliyan 50 yayinda bayanai ke cewa yanzu haka ‘yan bindigar sun sauya farashin zuwa miliyan 30 gabanin sakin yaran.

Har zuwa yanzu dai babu wani yunkuri daga bangaren gwamnatin jihar ta Neja da ke nuna za ta tallafa wajen kubutar da daliban Islamiyyar ta kowacce fuska kama daga amfani da karfin iko ko kuma biyan kudin fansar kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.


Post a Comment

0 Comments