Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dattawan Sabon Layin Kara Sun Jinjinawa Farfesa Adamu Gwarzo Bisa Gina Ajujuwa 11 Da Burtsatse 16

Daga Ali Kakaki Shugaban Dattawan Sabon Layin Kara dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, Alhaji Halliru Muhammad Tukur, ya ...


Daga Ali Kakaki

Shugaban Dattawan Sabon Layin Kara dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, Alhaji Halliru Muhammad Tukur, ya jinjinawa shugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, bisa gina ajujuwan karatu guda goma sha daya da burtsatsen ruwa guda sha shida a garin. 


Shugaban Dattawan ya yi wannan jinjinar ne a madadin al'ummar Sabon Layin Kara a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a harabar makarantar da Farfesa Abubakar Gwarzo ya gina ya kuma sadaukar ga al'ummar garin. "Kalmomi sun yi karanci wajen bayyana murnar mu da godiyarmu bisa wannan kyakkyawan aiki, amma zamu ci gaba da rokon Allah ta'ala da ya ci gaba da kare shi da shiga dukkanin lamuransa", ya tabbatar. 


"Har wala yau zamu ci gaba da rokon Allah ta'ala da ya ci gaba da yiwa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo albarka, sannan kuma ya sanya mahaifinsa, Marigayi Alhaji Garba a Aljannah Firdaus", Alhaji Halliru Muhammad Tukur ya jaddada. 


Ya kara da cewa; al'ummar Sabon Layin Kara suna matukar alfahari da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da ya zama dansu nagari kuma suna alfaharin mu'amala da shi saboda jajircewarsa wajen ci gaban al'ummarsa. 


Shugaban Dattawan ya ce samar da ajujuwan karatun zai taimaka sosai wajen bunkasa ilimi a yankin, a yayin da gina burtsatsen ruwan za su taimaka wajen rage radadin wahalar ruwa da ake fama da shi a al'ummar. 


"Muna rokon Allah ta'ala ya ci gaba da yi masa albarka domin ya ci gaba da wadannan ayyukan alherin. Allah kuma ya kare shi daga munanan ayyuka", ya yi masa addu'a. 


An gudanar da ayyukan guda biyu ne a karkashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo , kuma ana gab da kaddamar da ayyukan a mika shi ga gwamnatin Kano da kuma al'ummar. 

No comments